Kamfanin fasaha na google ya bayyana wata sabuwar mota daya kera maras matuki, kamfanin dai yayi nunin wannan fasaha daya kera a jiya litinin.
An dai kera wannan mota ne batare da wasu abubuwan da mutum ke bukata domin tukawa ba, kamar sitiyari, abin danna burki harma giya duk motar batada su, sai dai akwai abinda mutum zai iya dannawa domin juya akalar motar idan bukatar hakan ta faru. Amma motar nada duk sauran abubuwa da duk sauran mototoci keda su, idan aka ga motar baza’a taba cewa ba mutum bane ke jan akalar motar ba.
An dai kera motar ne da na’urori fasaha dadama, kamar su kamara domin ganin duk abinda ke faruwa, da kuma sensosi daza’a iya gane meke kusa da motar ko inda take.
Manufar kamfanin shine a nan gaba zai cire duk wasu abubuwan dake cikin motar domin baiwa fasinja gurin da zai iya barci kafin zuwa inda ya nufa.
Kamfanin dai zai cigaba da gwajin sabuwar motar akan tituna na musamman masu zaman kansu, kuma ya nuna cewar idan har komai ya tafi dai dai zai fara kera ire-iren motocin da ake dasu kamar su Toyota, Honda, harma da irin su Lexus. Kamfanoni da dama harma da wasu jami’o’i na kokarin fitowa da irin wannan fasaha, sai gashi google ne kamfani na farko daya fara fitowa da ita.
Your browser doesn’t support HTML5