Sabuwar Wayar Hannu ta Blackberry Classic

Sabuwar wayar Blackberry Classic

Kamfanin wayoyin hannu na Blackberry ya kaddamar da sabuwar wayarsa da aka jima ana jira, watau Blackberry Classic, wadda yake fata zata sake maidowa da kamfanin martaba da tasiri a kasuwannin wayoyin hannu, tare da janyo hankulkan masu amfani da tsoffin wayoyinsa.

Kamfanin Blackberry mai hedkwata a Canada, yace sabuwar wayar, wadda ta yi kama sosai da wayoyinsa da suka shahara a can baya, nau’in Bold da kuma Curve, yana da babbar fuska fiye da na baya, da baturi mai jimawa, da kiuma Apps masu yawa. Babban abin bambanci ma shi ne a yanzu, mai Blackberry Classic zai iya yin amfani da Apps na Android.

Kamfanin yace manhajar bude intanet dake jikin sabuwar wayar, watau Browser, saurinsa ya ninka na baya sau uku, watau kamar kiftawa da Bismillah mutum zai iya shiga ko bude intanet.

Shugaban kamfanin Blackberry, John Chen, yace sabuwar wayar Blackberry Classic, ta kuma maido da abubuwa da dama da aka cire a lokacin da aka bullo da wayoyi masu amfani da Blackberry 10 a 2012, watau aninai kamar na Menu, Back, Send da End, har ma da dan wurin da ake shafawa domin motsa allurer fuskar wayar daga kan wannan App zuwa wancan.

Chen yana kokarin mayarda kamfanin Blackberry zuwa ga asalinsa, watau kasancewar yana da aninai na harrufa da lambobi, kamar yadda aka gani a lokacin da aka kaddamar da Blackberry Passport, yanzu kuma ga Blackberry Classic. Watau dai, ba wai yana neman yin takara ne kai tsaye da abokan hamayya irinsu Samsung da Apple wadanda su wayoyinsu sun fi mayarda hankali kan amfani da yatsa wajen tabe-taben jikin fuskar wayar.