Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yana ikirarin galaba kan kotun kasa da kasa mai hukunuta laifuffukan yaki, bayan da mai gabatar da kara a kotun ya bada sanarwar dakatar da bincike kan laifuffukan yaki da aka aikata a yankin Darfur.
Da yake magana a yau Asabar a khartoum, shugaba Bashir yace al'umar kasar sun sami "galaba"kan kotun kasa da kasar da hkumomin kasar suka ki mika jami'an kasar da ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki a yankin Darfur ga kotun da ya kira ta "ta mulkin mallaka".
Yace kotun ta amince cewa ta "gaza" a yunkurin ta na auna bincikenta akansa.
A jiya jumma'a ce dai babbar mai gabatar da kara a gaban kotun Fatou Bensouda tace bata da sauran zabi "illa ta jingine bincike kan shugaba al-Bashir" ta karkata kudaden wajen wasu ayyuka na daban.