Sati Daya Bayan Barin PDP, Sanata Bagudu Ya Zamo Dan Takarar Gwamnan APC A Kebbi

APC

Kasa da mako guda a bayan da ya fice daga cikin jam'iyyar PDP, sanata Abubakar Atiku Bagudu ya zamo dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jihar Kebbi.

A bayan da aka shafe kwanaki biyu da rabi ana gudanar da zaben fitar da gwanin, sanata Atiku Bagudu ya doke sauran mutane 4 da suka yi takarar da shi da kuri'u masu yawan gaske.

Sanata Bagudu yace ba zai fuskanci babban kalubale a babban zaben da za a yi ba a saboda a cewarsa, yanzu sun farga cewa jam'iyyar PDP ba zata iya biyan muradun al'ummar jihar ba.

Sai dai kuma, sauran wadanda suka yi takara da shi din sun koka a kan cewa an yi magudi, kuma tun farko an shirya wannan zaben ne ta yadda zai fito a zaman dan takara.

Your browser doesn’t support HTML5

Sati 1 Bayan Barin PDP, Sanata Bagudu Ya Zamo Dan Takarar Gwamna Na APC A Kebbi - 2'58"