Rayuwa Ta Fara Komowa A Mubi, Amma Har Yanzu Akwai Gawarwaki A Kan Tituna

Fadar Mai Martaba Sarkin Mubi Bayan Da Sojojin Gwamnati Suka Shiga Garin, 30 Nuwamba, 2014

Rayuwa ta fara gudana a garin Mubi na Jihar Adamawa, a bayan da dakarun Najeriya suka kara karfafa tsaron wannan gari bayan kwace shi daga hannun ‘yan Boko Haram.

Wakilinmu Ibrahim Abdeulaziz na cikin wadanda suka zaga garin tare da dakarun tsaro, inda 'yan tireda a kasuwar Mubi suka fara bude shagunansu tare da bayyana godiya ganin irin sabbin matakan da ake dauka na tsare garin. Wata mace 'yar kasuwa ta bayyana gamsuwa tare da kira ga jama'a da su komo garin na Mubi.

A fadar Sarkin Mubi wakilin namu ya gano an ciccire tutocin da 'yan Boko Haram suka kafa ciki, sai dai har yanzu ba a ma fara tunanin gyara irin barna mai yawa da suka yi ba, inda suka farfasa abubuwa da yawa a cikin gidan.

Har yanzu akwai gawarwakin mutane da yawa a titunan cikin garin na Mubi, abinda ke haddasa fargabar barkewar cuta. Sannan kuma ga alamu na yaki a ko ina, kama daga gine-ginen da aka lalata, zuwa kwanson harsasai da abubuwan da aka kona a garin.

A Mararrabar Mubi ma, ko ina mutum ya duba zai ga alamun kazamin fadan da aka yi a tsakanin 'yan Boko Haram da sojojin gwamnati wadanda ke samun dafawar mafarauta da 'yan banga.

Your browser doesn’t support HTML5

Jama'a Sun Fara Komawa Garin Mubi A Jihar Adamawa - 3'57