Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Aminu Tambuwal, yayi watsi da ikirarin da wasu keyi cewa idan har ‘yan sanda sun karya doka wajen hana su shiga cikin harabar majalisar, su ma wakilan sun karya doka ta hanyar shiga da karfi.
Da aka tambaye shi ko bay a ganin cewa fitarsa daga jam’iyyar PDP da ta dora shi kan wannan kujera ne ya janyo hakan, sai Aminu Tambuwal yace, duk da cewa shi dan PDP ne, ai jam’iyyar ta tsayar da ‘yar takara a wancan lokacin, ba ta goyi bayan tsayawarsa ba ma.
Sannan yayi bayanin dalilan janyewarsa daga cikin masu takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Yau alhamis kuma jam’iyyar APC zata tsayar da wadanda zasu yi mata takarar gwamna, amma a Jihar Neja, akwai kura. Wani wanda yace ya koma APC daga PDP tare da mutane dubu 10, Alhaji Mustapha Aliyu Wushishi, yace ya biya kudin takara, amma kuma an hana shi. Sai dai sakataren tsare-tsaren APC a Jihar Neja, yace ba su ma san ko shi wanene ba, domin babu sunansa a rajistar jam'iyyar a karamar hukumar da yake ikirarin yayi rajista.
Mutane 3 ne suke takarar neman tsayawa jam’iyyar APC a zaben fitar da gwanin na yau a Jihar Neja
Your browser doesn’t support HTML5