WASHINGTON, D.C —
A hirar da yayi da Muryar Amurka, Hassan ya bayyana yadda yake amfani da wakokinsa wajen fadakarwa akan matsalolin yammacin Afirka, musamman Janhuriyar Nijar.
Hassan yace “ina yi, kuma zan cigaba da yi. Domin a halin yanzu, akwai sabon fefen dana fiddo, akan hadin kai a Nijar.”
“Akwai wata waka dana fiddo, ita kuma domin zaman lafiya ne a Najeriya. Domin abinda ke faruwa a Najeriya, yana ci mana tuwo a kwarya. Ina kuka kwarai da gaske. Ya kamata yanzu, magabatan Najeriya, a hada kai, domin a tabbatar da zaman lafiya”.
Hassan Bakari ya jaddada cewa Najeriya giwa ce a nahiyar Afirka, kuma lafiyarta nada nasaba da kwanciyar hankali a nahiyar baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5