Mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, yace babu hannun gwamnatin tarayyar Najeriya a ayyukan kungiyar Boko Haram kamar yadda wasu kie yada irin wannan jita-jita.
A lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sunusi na biyu, mataimakin shugaban ya roki jama'a da su guji jita-jita yana mai fadin cewa alhakin gwamnati ne kare rayuka da dukiyar jama'a, ba wani abu akasin haka ba.
Namadi Sambo yace a matsayinsa na Musulmi, dan Arewa, kuma a matsayin sauran Musulmi 'yan Arewa manya dake rike da cibiyoyin tsaro na Najeriya, kamar ministan tsaro, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sufeto janar na 'yan sanda, babu ta yadda za a iya hada baki da su domin a cuci arewa da mutanenta.
Ya roki jama'a da su hada kansu, su kuma hada kai da jami'an tsaro wajen shawo kan wannan masifa dake addabar yankin arewa.
Your browser doesn’t support HTML5