Shugaban kungiyar magoya bayan ‘yan wasan motsa jikin na Najeriya, Rafiu Ladipo, yayi kira da, a dauki matakan da suka dace domin kada a maimaita abun da ya faru, bayan da Super Eagles suka gaza cin wasansu na samun guri a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Kungiyar Super Eagles dai na bukatar samun nasara a wasan da sukayi da Bafana Bafana amma hakan yaci tura, Zakarun Afirkan dai sunyi kunnen doki 2-2 a wasan.
Lapido dai yace, “Ranar laraba ranace data shiga tarihin wasan kwallon kafar a Najeriya, musammamma ga ‘yan kasa magoya bayan wasan. Ranace da muke da damar samun tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka, abin bakin ciki kuma ‘yan wasan mu suka jefamu cikin makoki.”
Yakuma kara da cewa, “wannan abin cibaya ne ga kwallon kafar a Najeriya, kuma ina kara cewa dole a dauki matakai kan lamarin.”
Lapido ya soki lamarin ‘yan wasan inda yanuna cewa rashin kishin wasan a zukatansu da kuma kira ga afara shirye-shirye da wuri na gasar cin kofin nahiyar Afirka dama gasar cin kofin kwallon duniya maizuwa ta shekarar 2018.
Your browser doesn’t support HTML5