WASHINGTON, DC —
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta dawo da dan wasan baya Jeremy Mathieu da dan wasan tsakiyar fili Rafina daga hutun raunuka, domin samun damar buga wasan La Liga tsakanin Barca da Sevilla.
Mathieu dai ya share makonni uku a gefen fili biyo bayan rauni da yaji a kafarshi ta dama, lokacin da Barcan ta sha kashi da ci daya da babu, a karawa da Celta Vigo, shi kuma Rafina wata tsoka a kafarshi yajiwa ciwo a wasan da ya dokawa kasarshi.
Shina Andres Iniester ya dawo kungiyar har ya fara wasannin atisaye, amma har yanzu likitoci basu bashi karfin gwiwa ya cigaba da wasa ba. A halin yanzu dai, kungiyar Real Madrid ce a kan teburin La ligan, inda ta baiwa Barca maki biyu kacal, bayan doka wasanni 11.
Your browser doesn’t support HTML5