Wani mazaunin garin wanda baya so a bayyana sunansa yace “abunda gwamnati da take yi, yanzu sune suke yi. Suna zartas da hukunci, da karbe ayyukan asibiti, da sojoji da ‘yan sanda.”
Wannan na zuwa ne a lokacin da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ke cigaba da raba kayan tallafi ga wadanda suka kauracewa gidajensu su sama da 20,000.
Alhaji Muhammad Kanal, shine babban jami’in hukumar NEMA dake kula da arewa maso gabashin Najeriya “akwai shinkafa, da gero, da hantsi, da dawa da masara. Akwai kayan kwanciya, akwai gidan sauro, akwai bokitin wanka sa sauransu.”
Yayinda wannan ke faruwa, wasu gwamnoni sun fara nuna tababa game da batun yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Najeriya, da mayakan Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5