Ko shakka babu shugabanin Ecowas na nan na daukar mataki don ganin cewa an kawo karshen rigingimu da ta’addanchi na 'yan boko haram da ke faruwa a kasar najeriya.
Da yake bayani kuma da yawun shugaban kasar Ghana kuma ciyaman na kungiyar Ecowas, Dr. Mustapha Ahmad mai ba shugaba shawara akan lamaran yau da kullum, yace akwai matakai da aka dauka bayan zaman farko da aka yi Na gaggawa akan zancen tsaro a nan yammacin afrika mussamun akan zancen boko haram da ta’addanci a kasar mali. yace dalili Kenan da sa aka dau matakai inda aka gayyato kasashe makwabta najeriya da kasar mali don saboda a magance wadannan rigingimu da ke faruwa na ta’addancin boko haram da kuma ta’addanchi a kasar mali.
A nasa bangaren kuma shugaban kasa John Damani Mahamman ya dau alwashin cewa a karkashin jagorancin sa, Ecowas za ta ci gaba da bai wa najeriya gudunmuwa wajen yaki da 'yan boko haram.
Your browser doesn’t support HTML5