‘Yan aware masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine sun harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar sojin Ukraine, inda sojojin gwamnati 14 ne suka rasa rayukansu, a cikinsu harda wani Janar.
WASHINGTON, DC —
Shugaba mai rikon gado Oleksanda Turchinov ya gayawa majalisar kasar Alhamis dinnan cewa an kashe sojoji 14 a lokacin da “yan ta’adda” suka yi amfani da roka wadda ake harbawa akan kafada, wajen kaiwa jirgin hari a kusa da birin Slovyansk dake hannun ‘yan aware.
A cikin wadanda aka kashe, harda Janar Sa-hi Kul-chit-ski, shugaban dakarun tsaron Ukraine, wato Ukraine National Guard wanda ke daukar nauyin ayyukan zaman lafiya da horaswa na musamman.
Da safiyar yau ne, wani shugaban ‘yan awaren yace kungiyarshi na rike masu sa idanu daga Turai su hudu, wadanda suka bace tun ranar Litinin.
Vya-ches-lav Pono-ma-rev, wanda ya kira kanshi “mai unguwar Slovyansk” yace masu sanya idanun suna nan kalau, kuma wata kila a sako su nan bada jimawa ba.