Musa Omaku na wata kungiyar kare muradun kabilar Alago yace ‘yan Ombatse na kabilar Eggon daga Tudun Adabu suka shiga Adabu da Obi su na kashe-kashe da kone-kone
A nasu bangaren, ‘yan kabilar Alago sun ce babu ruwansu da abubuwan da suka faru, haka kwatsam ‘yan kabilar Eggon daga Tudun Adabu, suka far ma garin Adabu suka karkashe ‘yan kabilar Alago, suka kona gidajensu, sannan suka shiga garin Obi, inda suka sake aikata wannan danyen aiki.
Musa Omaku na wata kungiyar kabilar Alago, yace abinda ya faru shi ne a ranar alhamis, sojoji a garin Obi sun samu labarin cewa akwai wasu ‘yan kungiyar Ombatse ta kabilar eggon dake kan hanyar zuwa wurin wani rikici a Awe, sai suka kama biyu daga cikinsu, suka yi kokarin tafiya da su Lafia, hedkwatar jihar. Yace jin wannan sai ‘yan kabilar Eggon suka tare hanya suka fara far ma ‘yan Alago.
Yace a cikin daren alhamisar, ‘yan kabilar Eggon daga Tudun Adabu sun dira kan garin Adabu, inda ‘yan kabilar Alago ke zama, suka kona gidaje tare da kashe mutane, daga nan suka zarce zuwa garin Obi, inda nan ma suka far ma unguwannin ‘yan Alago.
Musa Omaku, yace akasarin ‘yan kabilar Alago sun gudu zuwa garin Keana domin tsira da rayukansu, kuma a nan din ma, akwai rade-radin cewa ‘yan kabilar ta Eggon su na da niyyar kai musu farmaki a can inda suka nemi mafakar.
Ga dai cikakken bayanin wannan lamari daga bangaren su ‘yan kabilar Alago, kamar yadda Musa Omaku yayi bayani a hirarsu da Ibrahim Alfa Ahmed.

Your browser doesn’t support HTML5