Kwamitin Ahuwa Na Boko Haram Ya Ziyarci Maiduguri

'Yan jarida su na kallon makaman da sojoji suka ce sun kwace daga hannun mayakan Boko Haram a Maiduguri, Jihar Borno

Ministan ayyuka na musamman kuma shugaban kwamitin, Kabiru Tanimu Turaki, ya ce sun karu ainun da irin bayanan da suke samu a Maiduguri
Shugaban kwamitin da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kafa domin sasanta rigingimu da wanzar da zaman lafiya a arewacin Najeriya, ya ce ba zasu iya gudanar da wannan gagarumin aikin ba, muddin ba su fita daga Abuja sun zaga wuraren da ake fama da wannan fitina ba.

Shugaban kwamitin, kuma ministan ayyuka na musamman na Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki, yana magana ne a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a bayan da shi da 'yan kwamitinsa suka gana da gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, a gidan gwamnati.

Barrister Turaki, yayi wa al'ummar Jihar Borno jajen irin rayuka da dukiyoyin da aka yi hasara a wannan rikicin da ake yi.

Yace sun ga canji sosai a Maiduguri, domin akwai tsaro mai karfi a cikin gari, kuma mutane sun fara fitowa su na gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Yace wannan ya nuna cewa jami'an tsaro da gwamnatin jihar Borno da ta tarayya da duk masu hannu a wannan lamarin, sun dage sosai domin tabbatar da ganin an koma rayuwa irin yadda aka saba ta lumana da kwanciyar hankali a jihar.

Gwamna Kashim Shettima yace babban abin dake ba shi takaici game da wannan lamari shi ne yadda wasu mutane ala tilas suka bar gidajensu domin tsoron abubuwan da ka iya samunsu a saboda sun ki bin akidar wasu mutane, da kuma yadda ake kashe-kashe na rashin imani ma wasu.

Ga cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:

Your browser doesn’t support HTML5

Kwamitin Ahuwa A Maiduguri - 2:48