Za a yi amfani da wannan kudi ta hannun hukumar Kiwon lafiya ta Duniya domin sanya idanu da binciken wuraren da ake samun yaduwar cutar a Najeriya
Hukumar tallafawa kasashen waje ta kasar Canada ta ware kudei har dala miliyan 18, kimanin Naira miliyan dubu 2 da miliyan 790, domin tallafawa wajen yakar cutar shan inna ko Polio a Najeriya. Za a yi amfani da kudin wajen sanya idanu da bin diddigin cutar domin sanin wuraren da ya kamata amyar da himma da karfafa yin rigakafin.
Za a mika wannan kudin agajin ta hannun ofishin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya dake Najeriya.
Ofishin jakadancin kasar Canada a Najeriya, yace wannan kudin agajin, wani bangare ne na kudi dala miliyan 250 wanda ministan Hadin Kai Da Kasashen Duniya na Canada, Julian Fantino, ya bada sanarwar agajinsu a lokacin Taron kolin Kasashen Duniya Kan Rigakafi da aka yi a Abu Dhabi cikin watan Afrilu.
Akasarin wannan kudin za a yi amfani da shi ne wajen tallafawa yunkurin kawar da cutar Polio a kasashe guda uku inda ta yi katutu a duniya, watau Najeriya da Afghanistan da kuma Paklistan.