An Kai Farmaki A Kan Gidan Kurkukun Birnin Yamai

Sojoji su na gadin babban gidan kurkukun Yamai, a bayan farmakin da aka kai asabar, 1 Yuni, 2013.

Jami'an Nijar sun ce an kashe masu gadin kurkukun biyu, amma ba a san yadda fursunonin suka samu makamai, ko kuma idan wasu maharan daga waje suke ba
Jami'an gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun ce an kashe masu gadi su akalla biyu yau asabar a lokacin wani farmaki a kan babban gidan kurkuku na Yamai, babban birnin kasar.

Kakakin gwamnati, Marou Amadou, yace wani mai gadin guda daya ya ji mummunan rauni. Yace wasu fursunoni da dama da ake zargin su na da hannu a ayyukan ta'addanci, sune suka tayar da wannan fitina, kuma an sake kamo akasarinsu an maida gidan kurkukun.

Amadou yace an kaddamar da bincike domin gano yadda aka yi wadannan fursunoni suka samu makaman da suka kai farmaki da su.

Ba a san ko wasu maharan daga waje suke ba har ya zuwa yanzu.

Wannan farmaki ya zo mako guda kawai a bayan da wasu masu kishin Islama suka kai tagwayen hare-hare lokaci guda a kan wani barikin soja a garin Agadez da kuma wani kamfanin hakar ma'adinin Uranium a garin Arlit. An kashe mutane kimanin 20 a harin da aka kai kan barikin, akasarinsu sojoji.