Shugaban 'Yan Tawayen Seleka Ya Amince Akan Yin Zabe

Hoton Michel Djotodia kenann.

Shugaban ‘Yan Tawayen da suka kwace iko a janhuriyar Afirka ta Tsakiya ya amince akan wata shawara a yankin da zata mayar da kasar kan turbar demokradiyya.
WASHINGTON, D.C - Ministan yada labaran shugaba Michel Jotodia ya fada yau alhamis cewa Jotodian ya amince da duk shirye-shiryen da shuwagabannin yankin suka tsara a ganawa da sukayi a kasar Chadi a cikin makonnan.

An rufe ganawar jiya laraba, kuma shuwagabannin Afirkan sun ki daukar Jotodia a matsayin shugaban kasar Janhuriyar Afirka ta Tsakiya. Sun yi kiran kafa gwamnatin rikon kwarya da zata rike kasar na watanni 18 kafin ayi zabe.

Kungiyar ‘yan tawaye ta Seleka ta tunbuke shugaba Francois Bozize daga mulki ran 24 ga watan Maris.