Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniyar ya ce za a bukaci rundunoni biyu daban-daban a kasar Mali, rundunar mayaka da ta kiyaye zaman lafiya
WASHINGTON, DC —
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce za a bukaci rundunonin sojojin kiyaye zaman lafiya guda biyu daban-daban a kasar Mali, domin tsaron zaman lafiya da kuma yaki.
A cikin wani rahoton da za a gabatarwa Kwamitin Sulhun Majalisar, wanda Rediyon Muryar Amurka ya samu, Mr.Ban ya ce karshen ta dai wata rundunar kiyaye zaman lafiya mai karfin sojoji dubu goma sha daya ce za ta karbi aikin rudunar farko wadda ke karkashin jagorancin kasashen Afirka. Ya ce saboda barazanar da ake ci gaba da samu a kasar Mali har yanzu, kuma ya ce lallai ne a samu wata rundunar mayaka da shan kan ayyukan ta’addanci.
A cikin watan janairu aka tura sojojin Faransa kasar Mali domin su kori masu tsattsauran ra’ayin Islama wadanda su ka kama arewacin kasar a shekarar da ta gabata.
Rahoton na Mr.Ban a kan Mali ya kuma nuna cewa har yanzu mutane na cikin halin galabaita mai tsanani, inda wasu ‘yan kasar wadanda yawan su ya wuce miliyan hudu da dubu dari uku ke bukatar taimakon abinci tun shekarar da ta shige. Haka kuma ya bayyana matsalar tauye hakkokin bil Adama da cewa ita ma ta na tayar da hankali, musamman ma a arewacin kasar inda ake samun rahotannin kashe-kashen gilla, da fyade da kwasar ganima da kuma saka yara a aikin soja.