Zamu Kai Wa Sansanonin Sojan Amurka Farmaki - inji Koriya Ta Arewa

Ire-iren rokokin Koriya ta Arewa kennan.

Koriya ta Arewa tayi barazanar cewa zata iya kai farmaki akan sansanonin sojan Amurka dake a Guam da Japan don nuna jin haushin anfani da jiragen saman Amurka da aka yi a cikin rawar dajin hadin-gwiwa da aka yi tsakanin Amurka din da Koriya ta Kudu.
WASHINGTON, D.C - A yau ni wani kakakin rundunar sojan Koriya ta Arewa yake cewa dukkan wadandan sansanonin sojan na Amurka da suka hada da na rundunar sojanta na sama dake Guam da na sojanta na ruwa dake Okinawa ta Japan, wurare ne da rokokin Koriya din zau iya kaiwa gare su.

A cikin wa’adin Wata daya da ya gabata, Amurka tayi anfani da jiragen yakinta na sama samfurin B-52 don nuna alamar karfi a lokacin rawar dajin, abinda aka ce ya fusata hukumomin Koriya ta Arewa sosai, wanda har yassa suke barazanar maida murtani mai gauni.

Tun ba yau ba dai Koriya ta Arewa ta yi barazanar cesa zata kawowa Amurka farmakin nukiliya to amma ana jin da kyar in tana da isasshiyar fasahar yin hakan.

To amma kasashe da dama dake kawance da Amurka dake kusa da Koriya ta Arewa din na cikin fargabar ganin cewa su kam, tana iya kaiwa gare su.