Hukumar 'Yansandan Afirka Ta Kudu Ta Dakatarda Wasu Jami'anta

'Yan sandan Afirka ta Kudu a lokacin da suka kama wani ma'akacin mahaka ta Marikana.

Hukumar ‘yansandan Afrika ta Kudu ta dakatarda wasu ‘yansanda su takwas daga aiki saboda rawar da ake jin sun taka wajen daure wani mutum ga motarsu da jan sa akan titi.
A yau ne kwamishinan ‘yansandan Afirka ta Kudu, Riah Phiyega tace ko bayan wadanan ‘yansandan takwas, an kuma sauke wani kwamandansu daga aiki yayinda ake ci gaba da bincikar abinda ya faru.

Hotunan bidiyo da aka dauka sun nuna yadda ‘yansanda suka daure wannan mutum mai suna Mido Macia, 27, wanda dan kasar Mozambique ne kuma dan taksi, da ankwa ga jikin motarsu.

A hoton aka ga yadda suke jansa, mutane na ta rokonsu su tsaya, basu tsaya ba, karshenta Macia ya mutu yayinda yake hannun ‘yansandan.

Shugaban ATK Jacob Zuma yayi Allah-waddai da wannan abinda ‘yansandan suka yi, wanda yace “abin tada hankali ne, abin damuwa kuma wanda ba za’a amincewa ci gaban abkuwarsa ba.”