Amurka Zata Bada Tallafin Dala Miliyan 60 Ga Kungiyoyin Adawar Syria

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry a lokacin da yake ganawa da shugaban kungiyar adawar Syria, Moaz al-Khatib, Alhamis, Fabrairu. 28, 2013. (AP)

Amurka zata bada tallafin Dala milyan 60 ga kungiyoyin ‘yan adawa na kasar Syria. Taimakon zai hada da abinci, magungunna da sauran kayan agajin da basu hada da makamai ba.
A yau Alhamis ne sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry yake bayyana haka bayan tarukkan da yayi a birnin Rome na kasar Italiya, inda ya dada jadadda shirin Amurka na yin aiki da ‘yantawayen don a samar wa kasar zaman lafiya.

Daga cikin wadanda Mr. Kerry ya zanta da su a lokacin tarukkan dai harda shugaban majalisar mulkin Syria Mouaz al-Khatib, wanda tare ma da Kerry din suka bayyana a gaban ‘yanjardu.

Mr. Kerry yace daya daga cikin hujjojin da suka ingiza Amurka baiwa ‘yantawayen tallafi shine ganin yadda gwamnatin Syria, wacce ta fi s karfin soja, take anfani da karfin wajen azabatar da mutanen kasar ta Sham.