Karshen ta dai Chuck Hagel ya zama sakataren tsaron Amurka duk da kokarin da wasu 'yan Republican su ka yi na neman hana tabbatar da shi
WASHINGTON, DC —
Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri’ar tabbatar da nadin da shugaba Barack Obama ya yiwa Senata Hagel a matsayin sabon Sakataren Ma’aikatar tsaron Amurka.
A kuri’ar da ‘yan majalisar dattawan suka kada daren jiya Talata, masu goyon bayan sun sami rinjaye da kuri’u 58, wadanda basa goyon baya nada kuri’u 41.
Shugaba Barack Obama ya yaba da yadda ‘yan majalisar dattawan na Amurka suka kada kuri’ar amincewar da ya kira abinda yafi dacewa a lokacin da ake bukata.
Wata sanarwar da fadar shugaban Amurka ta White House ta bayar na bayyana Chuck Hagel a zaman tsohon soja mai kishin Amurka. Shi dai Chuck Hagel, tsohon dan majalisar dattawan Amurka ne mai wakiltar jam’iyyar Republican.