Yau Ake Kammala Taron Shugabannin Kasashen Musulmi

'Yan jarida na daukar hotunan mahallarta taron shugabannin kasashen Musulmi a birnin al-qahira a kasar Masar. Fabrairu 6, 2013.

A yau ne shugabannin kasashen Musulmi na duniya suka kamalla taron da suke a Misra, wanda kusan dukkan magangannun da aka yi a cikinsa sun ta’allaka ne akan rikicin kasar Sham (Syria).

Ana sa ran kowane lokaci daga yanzu wannan kungiyar, mai kasashe 57 a cikinta, zata fito da sanarwar karshen taron wacce zata yi kira da a nemi mafitar siyasa daga wannan tarzomar ta Syria wacce ta riga ta lakume rayukkan mutane sun kai dubu 60.

Amma, a cikin daftarin farko na sanarwar da zasu bada, anga cewa shugabannin kasashen Musulmin na dora laifin duk wannan rikicin da aka share shekaru biyu ana tafkawa ne akan shugaban Syria Bashar al-Assad.

Dam dai tun watan Agustan bara kasashen suka kori Syria daga cikinsu kuma tun wancan lokaci suka bada sanarwar dake la’antar shugaba Assad akan anfani da karfin tsiya akan mutanen kasarshi.