Rasha Ta Damu Da Harin Jiragen Saman Isra'ila A Kasar Syria

Wata motar yakin Isra'ila kennan girke a bakin iyakar Isra'ila da Syria.

Rasha tace ta damu matuka da jin cewa jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hari a cikin kasar Syria.

Ma’aikatar harakokin wajen Rasha tace idan har wannan labarin ya tabatta, to ba shakka Isra’ila ta karya hakkokin diyaucin kasar Sham, a matsayin kasa mai cikakken ‘yancin kanta, ya kuma sabawa dukkan ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya.

Ana dai samun rahottanin masu saba wa juna da suka hada da wanda su kansu hukumomin Syria suka bada, dake cewa jiragen Isra’ila din sun sako bama-bammansu akan wata cibiyar bincike ta soja dake kusa da birnin Damascus, har suka kashe mutane biyu.

To amma su kuma kafofin watsa labaran Isra’ila da yammacin Turai cewa suke jiragen isra’ila sun kai wannan farmakin ne a wani wuri na daban dake kusa da kan iyakar Syria da Lebanon.

Kuma sun ce harin an kai shine akan wani ayarin motocin dake dauke da makaman da suka hada da rokokin da za’a kaiwa Hezbollah, kungiyar dake adawa sosai da Isra’ila, wacce kuma mazauninta ke a Lebanon.