'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kan Kwambar Ado Bayero

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero

Jami'ai suka ce mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, bai ji rauni ba a lokacin da aka kai farmaki a kan kwambar motocinsa asabar din nan.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun kai farmaki a kan kwambar motocin daya daga cikin manyan shugabannin Musulmi na kasar, suka kashe mutane uku.

Jami'ai suka ce mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, bai ji rauni ba a lokacin da aka kai farmaki a kan kwambar motocin nasa asabar din nan.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari a birnin Kano, birni mafi girma a yankin arewacin Najeriya.

Wannan lamari ya faru ana saura kwana daya tak a cikia shekara guda da mummunan harin bama-bamai da harbe-harben da ya kashe mutane 184 a birnin na Kano. An dora laifin harin na bara a kan kungiyar nan ta Boko Haram.

Kungiyar ta Boko Haram tana ikirarin cewa tana gwagwarmayar bkafa dokokin Shari'a ne a fadin Najeriya, kasar da akasarin mutanen arewacinta Musulmi ne, yayin da Kirista suka fi rinjaye a kudu.