Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ke Italiya, sun nuna farin cikinsu da dawowar Zlatan Ibrahimovic kulob din.
Dan wasan mai shekaru 38, da haihuwa ya amince bisa yarjejeniyar watanni shida a kungiyar ta AC Milan, da kuma wata yarjejeniyar sabunta kwantiraginsa nan gaba idan har kwalliya ta biya kudin sabulu.
Zlatan dan kasar Sweden, kuma tsohon dan wasan Manchester United da LA Galaxy, ya zira kwallaye 42 a wasanni 61, lokacin da ya buga wa AC Milan, a shekarar 2010 zuwa 2012.
Ya kasance dan wasa mai zaman kansa (Free Agent) bayan da ya kammala kwantiraginsa da LA Galaxy ta kasar Amurka a watan Nuwambar 2019.
Yayin da yake hira da 'yan jarida Ibrahimovic, dan wasan gaban ya ce kungiyoyin da suka neme shi da ya buga musu wasa a yanzu da yake da shekaru 38, sun fi wadanda suka neme shi a lokacin da yake matashi dan shekaru 20 yawa.
Ya kuma ce har yanzu matsayinsa da ya tafi ya bari a kulob din AC Milan na nan daram domin zai daura daga inda ya ajiye.
AC Milan tana matsayi na 11 ne da maki 21, a teburin gasar Serie A, na kasar Italiya, inda aka shiga mako na 17 da fara gasar.
Facebook Forum