Gwamnatin Zimbabwe ta kafa dokar hana fita daga safe zuwa dare, tare da rufe daukacin harkokin sufuri sakamakon COVID-19.
Hukumomin kasar sun ce suna daukan matakan ne wadanda babu ranar dage su domin kokarin da ake yi na shawo kan cutar COVID-19 da ke karuwa a kasar.
Jami'an tsaro zasu tabbatar da cewa mutane sun bi dokar wacce ke aiki daga 6 na safe zuwa 6 na dare.
Zimbabwe, wacce ke kudancin Afirka, na da mutum sama da 1,800 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kana 26 sun mutu. Amma kwararru a fannin lafiya sun ce akwai yiwuwar adadin masu cutar ya haura haka.
Shugaban kasar, Emmerson Mnangagwa ya ce "ba za mu nuna gamsuwa ba, hakan na nufin sai an dauki tsauraran matakai wadanda za su tilasta takaita wasu ‘yancinmu na walwala.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam da masu sukar lamirin gwamnati, sun ce an saka matakan ne da nufin dakatar da zanga-zangar adawa da gwamnati da aka shirya za a yi a ranar 31 ga Yuli.
A ranar Litinin, Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi wa Afirka gargadi kan yadda cutar ke kara yaduwa a kasar.
Facebook Forum