Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN VOA: Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Katsina, Kaduna Da Zamfara - Mayu 18, 2024


Medina Dauda
Medina Dauda

Shirin Zauren VOA na wannan makon ya kawo muku tattaunawar da gwamnonin jihohin arewa maso yamma guda uku suka yi, wato gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, da Uba Sani na jihar Kaduna, da kuma Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Gwamnonin na daga cikin tawagar gwamnoni goma da Cibiyar Koyar da Dabarun Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta gayyata Washington a kwanan nan.

A yayin ziyarar da suka kai sashen Hausa na Muryar Amurka a Washington DC, gwamnonin sun tattauna kan batutuwa da suka shafi kalubalen tsaro da suke fuskanta a jihohinsu, da dai sauransu.

Saurari shirin cikin sauti:

ZAUREN VOA: Tattaunawa Ta Musamman Da Gwamnonin Jihohin Katsina, Kaduna Da Zamfara - Mayu 18, 2024
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG