Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga zangar Dalibai a Hong Kong Na Cigaba da Yaduwa


Dubban masu zanga zanga suka toshe hanyoyi
Dubban masu zanga zanga suka toshe hanyoyi

Dalibai da 'yansandan kwantar da tarzoma suna cigaba da fito na fito a Hong Kong yayin da zanga zangar da daliban suka fara na yaduwa

‘Yan sandan kwantar da tarzoma suna ci gaba da fito na fito da masu zanga zangar kare damokaradiya a birnin Hong Kong,suna harba barkonon tsohuwa yayinda zanga zangar ta bazu da safiyar yau Litinin.

A kalla mutane 26 suka ji rauni a tashin arangamar.

Zanga zangar ta bazu zuwa wata cibiyar kasuwawancin Causeway ta kuma ketare Mong Kok abinda ya zama babbar kalubala ga hukumomi har su iya shawo kanta ba.

Dubban mutane sun ci gaba da zanga zanga a kewayen babban ginin gwamnatin Hong Kong suka yi watsi da sakonnin da dalibai da kuma shugabannin masu rajin damokaradiyar suka aika suna kira garesu su ja da baya domin gudun kada ‘yan sanda su harbe su da harsashen roba.

Wani dalibi ya yi kira ga gwamnati ta maida hankali kan zanga zangar da aka shafe kwanaki ana yi.

Mutane da dama a cikin masu zanga zangar suna raira take bayan sun rufe fuskokinsu da abin kare iska mai guba.

An fara zanga zangar ne jim kadan bayanda babban jami’in birnin Hong Kong yace gwamnati zata kaddamar da wani sabon zagayen tattaunawa kan yiwa harkokin zabe garambawul. Sai dai bai bayyana lokacin da za a yi zaman ba.

Masu zanga zangar suna daga cikin jerin masu tada kayar baya suna neman Beijing ta janye hannunta daga harkokin tsohon yankin da Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka.

XS
SM
MD
LG