Firam Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce kasarsa ta samu zaman lafiya, bayan mako guda, na tashe-tashen hankulan da suka yi, da ya janyo sanadiyar mutuwar mutane 67, da kuma lalata wuraren addini da dama.
Yanzu haka, yana ƙoƙari ya dawo da kwanciyar hankali.
A wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar, Abiy yace, ya na cikin mutukar damuwa akan yawan hare-hare.
"Wannan wata jarabawa ce, da ke nuna idan Habashawa ba su yi aiki tare ba, kuma da haɗin kai, hakan zai iya zame mana yanayi mai kunci, da ban tsoro," in ji shi a cikin harshen Amharic.
Facebook Forum