A yau juma’a Shugaban alkalan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Tade Azeez ya yi kira ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta dauko babban kocin da zai jagoranci kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Super Eagles wanda zai canza wa kungiyar fasali daga waje a maimakon cikin gida.
Azeez ya yi wannan kira ne a wata hira da ya yi da mujallar NAN ta wayar tarho a Illorin babban birnin jahar Kwara.
Alkalin wasan ya ce, “dauko kocin daga wata kasa ne kadai zai magance matsalar hukumar kwallon kafa ta Najeriya tunda baza a iya raba kwac kwac din gida da harkokin neman na aljihu ba.”
Azeez ya kara da cewa yawanci ba a raba kwac kwac din na cikin gida da nuna banbanci tsakanin ‘yan wasa ba tare da la’akari da irin lahanin da hakan ke yiwa kungiyar ‘yan wasan ba.
Ya kara da cewa “idan kungiyar zata amince ta dauko jagoran kungiyar daga wata kasa, hakan zai taimakawa kungiyar kwarai kuma hakan zai sa hukumar tasan cewa ga adadin kudin da zata rika biyan kocin a kowane wat aba tare da abin ya kawo masu wani cece kuce ba.”
“Dukkan su kasuwanci kawai suke yi, kowannen su nada dan wasan da yake da shi a zuciya domin nemen kudi kuma haka suke tilasta wa ‘yan Najeriya amincewa da dan wasan kuma daga karshe haka bazata cimma ruwa ba, duk matsalar su Kenan.”
“ba ruwan su tantance kwararrun ‘yan wasan da za su wakilce mu, burin su kawai neman kudi, kuma a gani nay a kamata a matsayin sun a kwararru su san ban bancin neman kudi da kuma aikin koci”.
Kungiyar ‘yan wasan Super Eagles dai bata da wani tsayayyen koci tun daga lokacin da tsohon kocin kungiyar yayi mata murabus din bazata.
Ranar 20 ga watan Afirilun wannan shekarar ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ba mai ba kungiyar shawara Shaibu Amodu da Salisu Yusuf rukon kwaryar jagorancin kungiyar.