‘Yan sa’o’i kafin a fara kad’a kuri’u, an ji ‘karar fashewar wani abu a garin Maiduguri dake Arewa maso Gabashin Najeriya. Sai dai ba a tabbatar da abin da ya haifar da fashewar ba cikin gaggawa, amma mayakan kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a garin Maiduguri.
A can wani garin dake Arewa maso Gabashin Najeriyar, Geidam, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahotannin wasu hare-hare daga masu tsatsaurin ra’ayi a yau Asabar, lamarin da ya tilastawa iyalai barin gidajensu.
Daya daga cikin ‘yan garin da yake Magana ta wayar talho da Reuters ya ce “
Mun gudu, baki dayanmu da matanmu da yaranmu da kuma sauran daruruwan mutane
.” Ya ci gaba da cewa yanzu haka muna cikin daji muna ta gudu.
Jiya Juma’a shugaba Buhari ya ce za a samar da tsaro a dukkannin rumfunan zabe.
A wani jawabi da yayi wanda aka nuna ta talabijin a fadin kasar, Shugaba Buhari ya ce an dauki matakan tsaro a fadin kasar don zaben, ya kuma tabbatar da cewa mutane zasu kada kuri’a ba tare da wata fargaba ba.
Rikicin siyasa na zafafa a kasar yayin da ‘yan Najeriya ke shirin zaben sabon shugaban kasa da ‘yan majalissu. A lokacin yakin neman zaben su, jam’iyyar APC ta shugaba Buhari da babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun zargi juna da yinkurin yin magudi don canza sakamakon zabe.
Facebook Forum