Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a yi zabe karo na biyu cikin watani biyar a kasar Turkiya


A combination of file pictures shows leaders of Turkish political parties Prime Minister Ahmet Davutoglu of AK Party, (top L), Kemal Kilicdaroglu of the main opposition Republican People's Party (CHP), Devlet Bahceli of Nationalist Movement Party (MHP), S
A combination of file pictures shows leaders of Turkish political parties Prime Minister Ahmet Davutoglu of AK Party, (top L), Kemal Kilicdaroglu of the main opposition Republican People's Party (CHP), Devlet Bahceli of Nationalist Movement Party (MHP), S

An kamalla shirye shirye a rumfunan zabe a kasar Turkiya kuma yan takara sun yi yakin neman zabensa na karshe a jiya Asabar.

An kamalla shirye shirye a rumfunan zabe a kasar Turkiya kuma yan takara sun yi yakin neman zabensa na karshe a jiya Asabar, kwana daya kafin ayi zabe a kasar a karo na biyu cikin watani biyar.
Prime Ministan kasar Ahmet Davutoglu yayi kira ga magoya bayan jam'iyar sa ta adalci da raya kasa ko ci gaba, da ake cewa Justice and Develpoment da turanci, AKP a takaice da su fito yau Lahadi suyi zabe. Ya kuma baiyana amanar cewa jam'iyar sa ce zata zama zakara.
Babar jam'iyar masu hamaiya ta CHP itama tayi gangaminta a jiya Asabar.
Shugaban kasar Recep Tayip Erdogan ne ya bukaci ayi sabon zabe bayan da jam'iyar AKP ta sha kaye, tayi hasarar rinjayenta a zaben da aka yi a watan Yuni daya bada mamaki. A saboda haka Prime Minista Davutglo ya kasa kafa gwamnatin gamin gambiza da sauran jam'iyun masu hamaiya guda uku da suke da wakilci a Majalisar dakokin kasar.
Wannan ne karon farko cikin shekaru goma sha uku da jam'iyar AKP tayi hasarar rinjayejn da take da shi a mulkin jam'iyar siyasa guda daya.
Masu kididdiga sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar mutane zasu fito yau Lahadi da yawa fiye da zaben da aka yi a watan Yuni kila kusan kashi tamanin da shidda daga cikin dari na wadanda suka cancanci yin zabe su fito.
Wannan zabe zai tantance ko jam'iyar AKP zata kwato gundumomin data yi hasarasu a zaben watan Yuni ko kuma a'a. Majalisar dokokin Turkiya tana da kujeru dari biyar da hamsin. Jam'iya tana bukatar kujeru maitan da saba'in da shidda domin ta samu rinjaye.

XS
SM
MD
LG