Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Ci Gaba da Yaki Har Sai Anga Bayansu


Rundunar ‘yan Sandan jahar Kaduna sun kwato shanu 94, da Tumakai 45, da kuma makamai iri daban daban a wani samame da ‘yan Sandan suka kai wata mabuyar wasu barayi Shanu.

Kakakin ‘yan Sandan Abubakar Zubairu, ya shaidawa kafanin dilancin labarai na Najeriya cewa barayi sun ranta ana kare bayan da suka yi dauki badadi da jami’an ‘yan Sandan.

Ya ce an samu bindiga da albarusai da dama da wukake da kayayyaki fasa gida da kuma rigunan Sojoji a maboyar tasu, a kauyukan Katari, Jere, Chikawali da Akilibu duk akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rundunar ta ce zata ci gaba da yakar barayi Shanu har sai sun ga babu saura , kuma ta yabawa ‘yan sandan da namiji kokarin da suke yi.

XS
SM
MD
LG