Ana shirin gudanar da zanga-zanga a yau a birnin New York domin nuna bacin rai kan kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na batanci akan wasu kasashe.
Za a gudanar da zanga zangar ce yayin da ake hutun tunawa da fitaccen dan gwagwarmayan nan Martin Luther King Jr a duk fadin Amurka.
A kwanakin baya wasu kafafen yada labarai a Amurka suka ruwaito cewa Trump ya kwatanta nahiyar Afirka da Haiti a matsayin kasashen "kasakantattu."
A fadi hakan ne yayin da yake wata ganawa da wasu 'yan majalisar dokokin Amurkan kan batun shige da fice.
Kalaman na Trump sun janyo kakkausar suka daga sassan duniya musamman ma daga nahiyar Afirka.
Abokiyar aikinmu Grace Alheri Abdu, ta zanta da wani dan asalin Ghana mazaunin Amurka, Muhammadu Mada, wanda ya yi tsokaci kan kalaman da ake zargin Shugaba Trump da fada.
Latsa kasa domin sauraren hirar:
Facebook Forum