Ranar Alhamis ne ake sa ran za’a rantsar da shugaban kasar Burundi da aka zaba, Evariste Ndayishimiye, mako daya bayan rasuwar shugaban kasar mai barin gado Pierre Nkurunziza, a cewar kafafen yada labaran kasar.
A makon jiya ne kotun tsarin Mulki ta yanke hukuncin cewa a rantsar da shugaban da aka zaba ba tare da bata lokaci ba.
Jam’iyar CNDD-FDD ce ta zabi Ndayashimiye da ya gaji Nkurunziza.
Ya yi nasarar samun kuri’u kashi 60 cikin dari a zaben na watan Mayu, wanda jam’iyar adawa da bata yi nasara ba ta yi zargin cewa, ya na cike da magudi.
Ndayashimiye zaiyi wa’adin shekara 7 ne kafin ya tsayawa takara a sake zabar sa.
Facebook Forum