Shugaban komitin kula da harkokin makamashi da wutar lantarki a majalisar wakilai Aliyu Magaji Da'u, daga mazabar Birnin Kudu da Buji a jihar Jigawa ne ya tabbatar da hakan a wata zantawa da ya yi da manema labarai akan batun samar da wutar lantarki daga Mambila.
Da ya ke bayani, Honarabul Aliyu Magaji Da'u, ya ce babu wani abu da ya wakana a shekarun baya a kan wannan batu na samar da wutar lantarki har megawat sama da dubu uku daga Mambila a Jihar Taraba.
"A rubuce kawai batun yake kuma a hannun 'yan boko wadanda ke birnin tarayya Abuja, saboda duk lokacin da ake wannan kwarmaton a kan wutar lantarki na Mambila, ba ayi komai ba sai da gwamnatin Buhari ta zo, alhali a wannan makon gwamnan jihar Taraba ya bada takardar amincewa da filin da gwamnati ta ke nema domin yin wannan aiki" a cewar Honarabul Magaji.
Honarabul Aliyu ya kuma kara da cewa, duk da himma da bukatar shugaba Buhari, ba za a gama wannan aikin a wannan lokacin ba, amma kwamitinsa na wutar lantarki zai yi bincike a kan kudaden da aka dade ana cewa ana fitarwa domin wannan aiki.
Tsohon shugaban kamfanin wutar lantarki na Kaduna, kuma mai ba Ministan wutar lantarki shawara, Idris Mohammed Madakin Jen, ya ce gaskiya ne ba a fara wannan aiki ba sai yanzu. Amma duba da irin kwazo da gwamnatin Buhari ke nunawa, za a iya gama aikin kafin shekaru 10 da aka diba na wa'adin kammala aikin.
To sai dai duk da cewa saura shekaru uku wa'adin wannan gwamnatin ya kare, jama'a za su sa ido tare da kyakkyawar fatan ganin an kammala aikin, domin a shawo kan matsalar rashin wutar lantarki a kasa.
A saurari rahoto cikin sauti daga Abuja a Najeriya.
Facebook Forum