Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Ci Gaba Da Aiwatar da Takunkumi Kan Rasha-Nuland


Mai magana da yawun ma'aikatar harakokin wajen Amurka, Victoria Nuland
Mai magana da yawun ma'aikatar harakokin wajen Amurka, Victoria Nuland

mataimakiyar sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace ba za a dage takunkumin da aka sawa Rasha ba sai an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin Ukrraine baki daya.

Wata babbar jami’ar diplomasiyar Amurka tace za a ci gaba da aiwatar da takunkumin da aka kakabawa Rasha sabili da rawar da ta taka a rikicin kasar Ukrain har zuwa lokacin da zata mutunta yarjejeniyar da aka cimma. Mataimakiyar sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland ta kuma yi gargadi jiya asabar cewa, Moscow zata fuskanci takunkumi da suka fi na yanzu tsauri idan ta sake keta yarjejeniyar.

Nuland ta bayyana haka ne a Kyiv babban birnin kasar Ukraine, a wajen wani taron jami’an siyasa da kuma ‘yan kasuwa na kasashen ketare.

Tace idan aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Minsk baki daya, da ta hada da mutunta diyaucin Ukraine da ya shafi kan iyakarta, daga nan zamu fara janye wadansu takunkumin.

Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai suna zargin Moscow da goyon bayan ‘yan ta’awaye masu ra’ayin Rasha da suka shafe watanni goma sha bakwai suna tada kayar baya a gabashin kasar Ukrain, suka kuma kakabawa Rasha takunkumi da dama da nufin hanata bada tallafin soji da kuma wadansu gudummuwa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG