Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Kyale 'Yan Kallo Su Ci Gaba Da Busa Algaitar Roba


Vuvuzela
Vuvuzela

Masu shirya gasar cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a Afirka ta Kudu sun ce ba zasu haramta shiga da ko kuma busa karamar algaitar robar nan da ake kira Vuvuzela ba duk da korafin da 'yan wasa da masu telebijin keyi.

Masu shirya gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya a Afirka ta Kudu sun ce ba zasu haramta algaitar nan ta roba da ke kira "Vuvuzela" ba, duk da korafe-korafen da ake yi cewa su na cikawa mutane kunne.

Masu koyar da 'yan wasa, da 'yan wasan kansu da kuma masu kallon wannan gasa a telebijin, su na kukar cewa dubban irin wannan algaita da 'yan kallo ke busawa lokaci guda a yayin da ake wasa su na cika musu kunnuwa. An kamanta wannan kara ta algaitar da mamayen miliyoyin kudajen zuma.

Amma masu kare busa wannan algaitar "Vuvuzela" sun ce ai wani bangare ne na wannan gasa a Afirka ta Kudu.

Ko ta ina mutum ya leka a Afirka ta Kudu zai ga jama'a, baki da 'yan kasa, su na busa wannan algaitar roba wadda karar dubbanta ta yi kama da karar kudar zuma.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG