Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na kulob din Manchester United Yaya Toure yayi yunkurin murabus daga buga wa kulob din kasa da kasa na Ivory Cost wasa.
A cikin satin nan ake sa ran cewar dan wasan zai bayyana ra’ayinsa na ko zai cigaba da bugawa Ivory Coast din wasan kasa da kasa ko kuma a’a.
Dan wasan na cikin kidan Manchester ya bayyna shawarar sa ta cewar a shirye yake yabi dan uwansa Kolo, wajan yin murabus daga buga wasan kasa da kasa domin samun cikakkiyar natsuwa da kuma mayar da hankali sosai akan kulob din sa.
Kolo dai ya yanke shawarar sa ne a fili cikin watan fabarairu, bayan hada hannu da yayi da Yaya Toure wajan taimakawa Ivory Cost a gasar lashe kofin nahiyar Afirka.
“Ina ganin na cimma burina,” a cewar Yaya Toure. Dan wasan ya bugawa kasar sa wasa har sau 91, ya kuma kara da cewar “zan jira zawa wasu ‘yan kawanaki kadan kafin in yanke shawarar abinda zanyi nan gaba”.kuma lokaci ya fara karatowa da zaratan ‘yan wasa matasa zasu fito kuma ya kamata mu barsu su taso.