Kuma da yawan su, suna rikidewa su zama ‘yan siyasa duk da kokarin da suke yi na samun daidaito da sabuwar rayuwar da suka samu kansu a ciki.
‘Yan African da suka yi kaura zuwa Amurka yanzu haka suna da kaso mai tsoka a cikin adadin mutanen dake kasar, kuma adadin nasu sai karuwa yakeyi tun daga shekarar 1970.
Musali a shekarar 2013 akwai ‘yan Africa da yawan su ya kai miliyan 1.8 dake zaune cikin Amurka, wanda wannan kari ne babbab idan aka kwatanta adadin da na shekarar 1970 dake da mutane dubu 80.
A wani binciken da aka gudanar a shekarar 2015 wanda cibiyar bincike da ake kira PEW RESEARCH CENTER SURVEY ta gudanar, tace kusan ‘yan Africa miliyan biyu ne da aka haifa Amurka ke zaune cikin kasar.