A yau za'a cigaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun turai Uefa Champion League, na shekarar 2018/2019 zagaye na biyu cikin karawa ta biyu a matakin kifa daya (Nockout).
Kungiyoyi guda hudu ne zasu kara inda Paris-Saint German, zata karbi bakoncin Manchester United, sai kuma FC Porto, su barje gumi da Roma.
A wasan farko da kungiyoyin sukayi PSG taci Manchester United a Ingila 2-0, ita kuwa Roma a Itali ta doke Porto ne daci 2-1.
Za'a fara wasan ne da misalin karfe tara na yammaci agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Kasar Ghana.
A wasan da aka buga a ranar Talata kuwa, Ajax tayi waje rot da Real Madrid bayan da ta lallasa ta daci 4-1, a Santiago Bernabeu inda take da jimillar kwallaye 5-3, bayan da Real a karawar farko ta shata 2-1 a gidanta a watan Faburairu 2019.
Ajax ce kungiyar farko da ta ci kwallo hudu a Santiago Bernabeu, tun bayan 2015 lokacin da Barcelona ta doke Real da ci 4-0 a wasan LaLiga ranar 21 ga watan Nuwambar 2015.
Rabon Real Madrid ta kasa kai wasan daf da na kusa da na karshe tun bayan shekara tara a gasar ta Champions League.
Ita kuwa Ajax wannan ne karon farko da ta kai wannan matakin tun a kakar 1996/1997, kimanin shekaru 22.
Sai dai kungiyar ta Netherland tana da kofin Zakaraun Turai guda hudu a tarihi.
A daya wasan kuwa Tottenham Hotspur ce ta samu nasara akan Borussia Dourtmund daci 1-0 jimillar kwallaye 4-0 a cikin karawa biyu da sukayi.
Facebook Forum