Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau 'Yan Jarida A Mozambique Za Su Fara Biyan Kudin Rajista Mafi Yawa A Duniya


 Shugaban Mozambique Filipe Nyusi
Shugaban Mozambique Filipe Nyusi

Daga yau a Mozambique dan jarida dake yiwa jaridar kasar aiki zai biya $3,500 idan kuma jaridar waje ce zai biya $8,300, kuma duk wanda zai kafa sabon gidan rediyo sai ya biya $35,000

Daga gobe Labara, 'yan jarida dake aiki a kasar Mozambique za su fara biyan abin da ka iya zama kudin rajista mafi yawa a duniya.

Wannan kudin rajistar dai ya sha suka, ta yadda ma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ke kiran kudin da "abin da ya wuce hankali," sannan ita kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ke cewa hakan zai sa 'yan jarida su kasa aikin bayar da labarai a Mozambique.

Duk wani wakilin kafar labaran kasar waje da ke aiki a wannan kasa ta kudu maso gabashin Afirka, zai rika biyan dala $8,300 duk shekara, kuma duk wani sabon gidan rediyo na kasa zai biya $35,000 na rajistar kafa shi. 'Yan kasar da ke wakiltar kafafen labaran ketara za su rika biyan dala $3,500 duk shekara a wannan kasar da adadin abin da ta ke samarwa bai wuce dala $1,200 a shekara daga kowani mutum guda ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG