A cewar wakilnmu ranar 28 ga watan Nuwamba na 2011 Shugaban Janhuriyar Nijar Issoufou Muhammadou ya jagoranci kafa matatar man fetur ta Janhuriyar Nija da ke Damagaram, wato yau shekaru hudu Kenan, amma talakawa na cewa babu abin da matatar man ke tsinana masu.
Wani shugaban kungiyar matuka motocin haya na tasi mai suna Gamace Muhammadu y ace cuwa-cuwa ce ta hana matatar man amfanar talakawan Janhuriyar Nijar. Ya yi takaicin abin da ya kira kasa fitowar da magabata su ka yi su ce wani abu. Ya yi zargin cewa yanzu babu wanda ya san adadin man fetur din da ake fitarwa daga kasar.
Haka zalika wakilinmu ya samu jin ta bakin wasu ‘yan kasar ciki har da Banani Usaini wanda ya ce babu wani dan Nijar da zai ce ga wani abun da ya amfana da shi sanadiyyar man fetur. Haka zalika wani dan tasi mai suna Mamman Sani ya ce a matsayinsa na dan tasi ya san irin wahalar da su ke sha game da mai saboda tsananin tsada.