Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau An Saki Dariye Da Nyame


Former Gov Nyame released
Former Gov Nyame released

An saki tsoffin gwamnonin ne yau dinnan Litinin, watanni kadan bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi musu afuwa.

Hukumomin gidan yarin Kuje a Abuja babban birnin Najeriya sun saki tsohon gwamnan Jihar Taraba, Rabarand Jolly Nyame da tsohon gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye.

An saki tsoffin gwamnonin ne yau Litinin, watanni kadan bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi musu afuwa.

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame hukuncin daurin shekara 14 a gidan kaso bayan ta same shi da laifin yin sama da fadi da kudi da yawansu ya kai naira miliyan 250.

An saki tsohon Gwamna Nyame
An saki tsohon Gwamna Nyame


Kazalika an samu Dariye da laifin almundahanar N1.16 bn a shekarar 2018 inda a watan Yunin shekarar wata kotun Tarayya ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 14 bayan samunshi da laifukan da suka shafi zamba da almubazzaranci.

Sai dai afuwar da Shugaba Buhari ya yi musu ta janyo ce-ce-ku-ce a kasar, inda ake ganin matakin a matsayin karfafa wa masu sace kudin kasar gwiwa.

Daga Wakilinmu a shiyar adamawa da Taraba Lado Salisu Muhammad Garba.

XS
SM
MD
LG