A dai shekarar 1955 King ya samu daukaka, bayan da ya jagoranci wani borin kauracewa shiga motocin sufuri na Bas a kudancin birnin Montgomery dake jihar Alabama, lamarin da ya tilsatawa hukumomin birnin kawo karshen tsarin nan da ke kebe fasinjoji bakaken fata.
A kuma shekarun 1950s da 60s, King ya zama jigon fafutukar neman ‘yan cin da shahararren jawabinsan nan mai taken “ I Have A Dream” wanda ya ja hankulan miliyoyin mutane a lokacin da ya gabatar da shi a wani gangami ko kuma maci da aka yi a nan Washington a shekarar 1963.
A shekarar 1964 ya karbi lambar yabon nan ta zaman lafiya, ko kuma Nobel Peace Prize, a kuma shekararce shugaba Lyndon Johnson ya saka hannu a dokar nan da ta tabbatar da samar da cikakken ‘yan ci ga mutanen da ake nunawa wariya musamaman bakaken fata.
A ranar hudu ga watan Aprilun shekarar 1968 aka kashe King a birnin Memphis dake jihar Tennessee, a lokacin da ya je ya taimakawa bakaken fata masu kwasar shara a fafutukar da su keyi ta neman a daidaita musu albashin su da sauran ma’aikata.
A shekarar 1983 shugaba Ronald Reagan ya saka hanu a wata doka da ta umurci a rika ware duk ranar Litinin ta uku a watan Janairu a matsayin ranar karrama Martin Luther King, wanda aka haifa a ranar 15 ga watan Janairun 1929.