Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Zagaye Na Biyu Na Zaben Mali


Shugaba Ibrahim Bubakar Kaita da Sumaila Cisse (Sise).
Shugaba Ibrahim Bubakar Kaita da Sumaila Cisse (Sise).

Yau ake harmar gudanar da zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar Mali tsakanin Shugaba Ibrahim Bubakar Kaita da tsohon Ministan Kudin kasar Soumaila Cisse. To sai dai ganin yadda aka kai hare-haren ta'addanci a lokacin zaben baya, masu zabe ba tsaron kar hakan ya sake faruwa.

‘Yan Mali za su kada kuri’ar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a yau dinnan Lahadi, yayin da su ke fargabar yiwuwar sake fuskantar harin ta’addanci, kamar yadda su ka firgita a zagayen farko na zaben makonni biyu da su ka gabata, lokacin da hare-haren ta’addanci su ka kawo cikas a runfunan zabe da dama a kasar.

Ba kawai tunanin yiwuwar hare-haren ta’addancin da ka iya shafar zaben ke damun ‘yan Mali ba, amma har ma da yadda zaben zai yi tasiri kan yakin da ake yi da kungiyoyin mayaka, wadanda ke da alaka da al-Ka’ida da ISIS.

Ministan Tsaron Mali, Tiena Coulibaly, ya gaya ma Muryar Amurka cewa tuni gwamnati ta dau matakin tabbatar da tsaro a fadin kasar a yayin da ake gudanar da zaben, kuma gwamnati ta himmantu ga yaki da kungiyoyin mayakan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG