Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau ake jana'izar mawakiya Whitney Houston


Wani wuri da jama'a suke tunawa da Whitney Houston
Wani wuri da jama'a suke tunawa da Whitney Houston

Yau ake jana’izar fitacciyar mawakiya da ‘yar wasar fina finan nan wadda ta sami lambobin yabo ta Grammy Whitney Houston

Yau ake jana’izar fitacciyar mawakiya da ‘yar wasar fina finan nan wadda ta sami lambobin yabo ta Grammy Whitney Houston, a garin haihuwarta Newark dake jihar New Jersey, kusa da birnin New York.

Fitattun mawaka da ‘yan wasan fina finai zasu rufawa danginta baya wajen karrama ta da kuma yi mata rakiya ta karshe a majami’ar Hope Baptist inda Houston ta yi waka a kwaya lokacin tana budurwa.

Jiya jumma’a da yamma danginta suka halarci wani shirin jana’izar ganinta na karshe a gidan shirya jana’iza.

Mawakar da zasu yi waka a wajen jana’izar yau sun hada da Steve Wondor da Aretha Franklin, ana kuma kyautata zaton mijinta na da, mawaki Bobby Brown zai halarci jana’izar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG