Karawar ta faru ne biyo bayan shiga harabar masallacin da 'yansandan Israila suka yi suna neman wasu matasan Falasdinawa da suka kare kansu cikin masallacin daga inda suka dinga jifan 'yansandan.
Mahukuntan Israila sun yi anfani da barkonun tsohuwa sun tarwatsa matasan Falasdinawan.
Jordan kasar da take da iko akan masallacin ta yi tur da samamen da 'yansandan Israila suka kai cikin harabar masallacin tare da zargin Yahudawan da kai harin ba gaira ba dalili. Jordan ta zargi Israila da kokarin sake matsayin masallacin, wuri mai tsarki a Gabas ta Tsakiya.
Bisa ga shirin da aka yi Yahudawa na iya ziyartar masallacin amma ba zasu yi ibada ciki ba saboda gudun tada hankalin Musulmai masu sallah a masallacin.
An sake bude masallacin bayan rikicin na jiya Lahadi..
Cikin 'yan kwanakin nan ana samun karuwar tashin hankali saboda Musulmi sun hasala da yadda wadanda ba musulmi ba suke yawan kai ziyara masallacin. Abu na biyu da yake bata wa musulmi zai kuma shi ne kokarin da ake yi na barinYahudawa su yi sujada a harabar masallacin..
Wurin nada mahimmanci ga Yahudawa a matsayin wuri mafi tsarki garesu. Ga Musulmi kuma wurin shi ne wuri mafi tsari na uku a addinin musulunci bayan Makkah da Madina a Saudiya.